Akwai tsauraran matakan tsaro a harabar kotun daukaka kara da ke yankin Shehu Shagari, Central Business District Abuja, yayin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ke shirin yanke hukunci.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Jam’iyyar APC, PDP da LP ne ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
NAN ta ruwaito cewa, dukkanin hanyoyin da suka kai ga kotun daukaka kara, jami’an tsaro ne da dama, wadanda aka zabo daga hukumumi daban-daban, da suka hada da jami’an tsaro, ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da kuma Civil Defence.













































