Zabe: Dan Majalisar Tarayya Ya Kayar Da Dan Ganduje A Kotu

Abba Umar Ganduje
Abba Umar Ganduje

Kotun sauraren kararrakin zaben Majalisar Dokokin Jihar Kano, a ranar Talata, ta tabbatar da zaben Sanata Abdulkadir Jobe, na jam’iyyar NNPP, mai wakiltar mazabar majalisar wakilai ta tarayya, Rimin Gado, Dawakin Tofa, da Tofa a mazabar Kano.

NAN ta ruwaito cewa Abba Umar Ganduje na jam’iyyar APC, dan tsohon gwamnan Kano ne ya shigar da karar, yana kalubalantar nasarar Abdulkadir-Jobe na NNPP a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rimin Gado, Dawakin Tofa da Tofa, wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. , 2023.

Da yake yanke hukunci, kwamitin mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a I P Chima, ya yi watsi da karar, saboda rashin cancanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here