‘Yan majalisu a Najeriya sun rubuta wasika ga shugaba Tinubu kan sakin Nnamdi Kanu

'Yan majalisu, Najeriya, rubuta, wasika, shugaba, Tinubu, sakin, Nnamdi, Kanu, IPOB
Akalla ‘yan majalisar wakilai 50 ne a shiyyoyin siyasar Najeriya shida, karkashin wata kungiya da ke Kudu-maso-Gabas. Inda suka roki shugaba Bola Tinubu da...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Akalla ‘yan majalisar wakilai 50 ne a shiyyoyin siyasar Najeriya shida, karkashin wata kungiya da ke Kudu-maso-Gabas.

Inda suka roki shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara) da sashe na 107 (1) na Dokar Gudanar da Laifukan Shari’a, 2015.

An bukaci shugaban kasar ya yi amfani da dokar wajen sakin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, daga hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Karin labari: Kano: An dakatar da Alkalan kotu 4 da Magatakarda kan wasu laifuka

‘Yan majalisar da aka zaba a jam’iyyun siyasa daban-daban a wata wasika da suka aike wa shugaba Tinubu, mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Yuni, 2024, sun bukaci dan kasa na farko da ya fara shirin zaman lafiya don magance kalubalen rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Wasu daga cikin wadanda suka sanya hannu kan wasikar mai shafi uku sun hada da Obi Aguocha na jihar Abia da Ikenga Ugochinyere na jihar Imo da Afam Ogene na jihar Anambra, sai kuma Muhammed Jajere na jihar Yobe da Aliyu Mustapha na jihar Kaduna tare da Midala Balami na jihar Borno da sauransu.

Karin labari: Surukar mataimakin shugaban kasar Najeriya ta rasu

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar ta IPOB ya bayyana muradin sa na ganin an warware tuhume-tuhumen cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ke yi masa a gaban kotu.

Ya kuma yi tir da kashe-kashen da ake yi a yankin Kudu-maso-Gabas sakamakon yunkurin kungiyar IPOB na raba kabilar Ibo da Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here