Cikin Hotuna: Sarki Sanusi ya bukaci a hukunta wadanda suka kashe ’yan asalin Kano a Edo, ya bukaci matasa su guji daukar fansa

WhatsApp Image 2025 03 30 at 11.34.49 750x430

Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya bukaci hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki da su tabbatar an yi adalci ga ‘yan asalin Kano da aka yi wa kisan gilla a jihar Edo.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Idi a filin Idi na Kano da ke kofar Mata a ranar Lahadi, wanda ya samu halartar gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da mukarrabansa.

WhatsApp Image 2025 03 30 at 11.00.10 768x576

Da yake jawabi cikin matukar damuwa, Sarkin ya jaddada muhimmancin adalci wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Ya bayyana cewa “Bai kamata a bar wannan al’amari ya tafi ba tare da hukunta shi ba, dole ne a yi adalci domin a hana ci gaba da samunWhatsApp Image 2025 03 30 at 11.00.09 1 768x576 barazanar zaman lafiya.”

Karanta: Sufeto janar na yan sanda ya yi tir da kisan matafiya a Edo, ya ba da umarnin gaggauta yin bincike

 

Sarkin ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ya bukace su da su nemi hakkinsu ta hanyar halal da lumana.

WhatsApp Image 2025 03 30 at 11.00.11 768x432

A wani kakkausan gargadi ga matasan Kano, Sarkin ya hana daukar fansa, yana mai jaddada cewa ramuwar gayya haramun ce a Musulunci.

Ya kuma yi kira ga matasa da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, kuma su jajirce wajen ganin an zauna lafiya, yana mai jaddada cewa duk wani mataki na daukar fansa zai kawo cikas ga neman adalci da kuma dagula al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here