Sufeto-Janar na ‘yan sandam kasar nan Kayode Egbetokun, ya yi Allah-wadai da ta’addancin da ya faru a jihar Edo da ya kai ga kashe wasu matafiya da aka yi zargin masu garkuwa da mutane ne.
Harin wanda ’yan banga na yankin suka kai kan hanyar Uromi-Obajana, ya haifar da mummunan sakamako.
A wata sanarwa a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, mai taken IGP ya yi Allah-wadai da ayyukan ‘yan ta’adda a jihar Edo, ya ba da umarnin gaggauta bincike, da kuma tabbatar da doka da oda.
Wadanda aka kashe ‘yan Arewa ne da ke tafiya a cikin wata babbar mota da ake kyautata zaton mafarauta ne, an same su da bindigogi 19 na gida.
Sai dai ’yan banga da suka yi shakkun bayaninsu, suka sanya su a matsayin masu garkuwa da mutane.
Labari mai alaƙa:Yan sanda sun kama mutane 14 a Edo bisa zargin kashe matafiya 16 ‘yan arewa
A martanin gaugawa rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta aike da jami’anta zuwa ga al’ummar da lamarin ya shafa domin dawo da zaman lafiya.
“Ya zuwa yanzu, an kama mutane goma sha hudu (14) da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da aka fara farautar sauran wadanda ke da hannu a wannan aika aika,” sanarwar ta tabbatar.
Karanta har ila yau: Tinubu ya nemi a gaggauta kama waɗanda suka kashe matafiya a Edo
Domin tabbatar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba, IGP ya umurci mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar (FCID), DIG Sadiq Abubakar, da ya dauki nauyin lamarin.
IGP din ya kara da yin kira da a kwantar da hankulan jama’a, sannan ya bukaci ‘yan kasar da su ba da hadin kai wajen gudanar da bincike, yana mai gargadin a kan yin adalci.
Rundunar ‘yan sandan ta gargadi jama’a da su daina daukar doka a hannunsu tare da karfafa kai rahoton abubuwan da suka saba wa doka cikin gaggawa.