An dage zaman fara shari’ar tuhumar laifin amfani da Internet da ake yi wa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, sakamakon ƙalubalen da lauyanta, Ehiogie West-Idahosa (SAN), ya gabatar.
Ana gurfanar da Natasha kan tuhume-tuhume guda shida a ƙarƙashin dokar wadda aka yiwa gyara ta shekarar 2024, da gwamnatin tarayya ta shigar.
A ranar 30 ga Yuni aka gurfanar da ita a karon farko inda aka ba ta beli bisa amincewa da kanta.
Tuhumar na zargin ta yada bayanai marasa inganci da kuma barazana ta hanyar yanar gizo, da nufin ɓata suna, tayar da hankali, barazana ga rayuka da kuma kawo rikice-rikice.
Karanta: Ba zaki dawo aiki yanzu ba – Majalisar dattawa ta faɗawa Natasha
Daga cikin tuhumar akwai ikirarin da ta yi a taron jama’a a Ihima, Jihar Kogi, a ranar 4 ga Afrilu 2025, inda ta ce shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya umurci tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da su kashe ta a Kogi.
A cewar takardar tuhumar da babban daraktan gurfanarwa na tarayya, Mohammed Abubakar, ya shigar, Natasha ta kuma maimaita wannan magana a wani shirin talabijin, tana zargin Akpabio da Yahaya Bello da shirin hallaka ta.
Da aka dawo zaman shari’ar a yau, lauyan masu gabatar da ƙara, David Kaswe, ya sanar da kotu cewa sun shirya kiran shaidu, har ma sun girka talabijin a cikin ɗakin kotu domin gabatar da hujjojin bidiyo.
Sai dai lauyan kare, West-Idahosa, ya kalubalanta kan ikon kotun wajen sauraron shari’ar, yana mai cewa akwai amfani da ƙarfin ikon lauya na Babban Lauyan Ƙasa ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma, ya koka cewa ba a mika musu kwafen bayanan shaidun masu gabatar da ƙara ba.
Duk da hujjar Kaswe cewa wannan ƙalubale bai kamata ya hana ci gaban shari’ar ba, alkalin kotun, Mai Shari’a Mohammed Umar, ya bayyana cewa zai fara sauraron ƙalubalen da aka gabatar kafin ɗaukar wani mataki.
Saboda haka, kotun ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 20 ga Oktoba 2025 domin sauraron ƙalubalen da kuma fara shari’a idan an kammala.













































