Samar da ƴan sandan jiha hanya ce ta jawo rikici – Tsohon AIG Adisa Bolanta Tsohon

WhatsApp Image 2025 09 22 at 13.24.11 720x430

Tsohon mataimakin babban sufeton ’yan sanda (AIG), Adisa Bolanta, ya bayyana adawarsa ga ƙoƙarin kafa ’yan sanda na jiha a Najeriya, inda ya bayyana shi a matsayin “hanya ta jawo bala’i”.

Bolanta, wanda ya yi magana da manema labarai a Ilorin, Jihar Kwara, ya ce masu goyon bayan tsarin suna yin haka ne saboda son rai, ba wai don ingancin tsaro ba.

A cewarsa, matsalar ’yan sanda a Najeriya ba ta ta’allaka ne kan tsarin cibiyoyi ba, illa rashin kuɗaɗe, ƙarancin kayan aiki da kuma tsoma bakin ’yan siyasa fiye da kima.

Tsohon jami’in ya yi aiki a matsayin kwamishinan ’yan sanda a jihohi daban-daban ciki har da Oyo, Sokoto, Kebbi da Imo, tare da rike mukamin kwamandan makarantar ’yan sanda ta ƙasa a Kano.

Ya bayyana cewa mafita ita ce a inganta ɗaukar nauyin rundunar ’yan sanda ta tarayya tare da aiwatar da tsarin yan sandan cikin al’umma, maimakon rushewa zuwa matakan jiha.

Bolanta ya kuma soki hujjar cewa jihohi za su fi iya ɗaukar nauyin ’yan sanda, yana mai cewa da yawa daga cikin jihohi ma ba su iya biyan albashin ma’aikatansu ba sai da tallafin gwamnatin tarayya.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin Tarayya da na jihohi na tunanin kirkirar ‘Yan Sandan Jihohi

Ya ƙara da cewa, a zahiri, kusan kashi 70 cikin ɗari na jami’an ’yan sanda a kowace jiha ’yan asalin jihohin ne, don haka batun wakilcin cikin gida ba shi ne ainihin matsala ba.

Ya bayar da misali da shekarar 1982 lokacin da aka tura shi a matsayin jami’in farko a ofishin ’yan sanda na Ekpoma, inda aka samar musu da motocin Land Rover guda biyu da manyan motoci don aikin sintiri da jigilar jami’ai, tare da kayan aiki da mai na kowane wata.

A cewarsa, irin wannan tsarin ne ya inganta aiki a lokacin.

Dangane da tsarin yan sandan cikin al’umma ya ce mutane na yawan fahimta ba daidai ba. “Ba wai a sa su su sa kayan sanyi ba ne, a’a, sai dai su bayar da bayanai da shawarwari, domin suna da masaniya kan al’ummarsu fiye da kowa.”

Bolanta ya kuma yi tsokaci kan tsaro a lokacin zaɓe, inda ya ce rashin kyakkyawan tallafi da tsoma bakin ’yan siyasa na lalata amincin jami’an tsaro.

Ya yi jayayya da ra’ayin cewa jami’in ɗan sanda ba zai yi gaskiya ba ko da ya samu isasshen tallafi, yana mai cewa idan aka ɗauki nauyinsu yadda ya kamata, za su yi aikin su cikin gaskiya.

A ƙarshe, ya jaddada cewa tsaro hakki ne na kowa, yana kira ga al’umma da su rika ba ’yan sanda goyon baya da sahihan bayanai a kan lokaci. Haka kuma, ya shawarci matasa su rika yin sutura cikin kamala don guje wa cin karo da jami’an tsaro.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here