NAHCON ta rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar maniyyata aikin hajjin 2026 da kamfanonin jiragen sama

download 1

Hukumar kula da Alhazai ta Kasa NAHCON ta rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar maniyyata aikin hajjin shekarar 2026 da kamfanonin jiragen sama, tare da umartar su da su bi ka’idojin aiki da jadawalin da aka tsara domin gudanar da aikin yadda ya kamata.

Shugaban hukumar, Ambasada Isma’il Yusuf Abba, ya bayyana a wajen rattaba hannun cewa wannan muhimmin mataki ne da ke nuna shirye-shiryen da aka kammala domin aikin hajjin 2026.

Hakan na cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da wayar da kan al’umma na hukumar Shafi Mohammed ya sanyawa hannu a ranar Laraba a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa aikin hajji na da iyakacin lokaci, don haka yana bukatar cikakken hadin kai da tsari domin tabbatar da an kai maniyyata zuwa kasar Saudiyya tare da dawo da su cikin lokacin da aka kayyade.

Hukumar ta gargadi kamfanonin jiragen sama da cewa bin yarjejeniyar ba zabin kai ba ne.

Ta ce duk kamfanin da ya yi aiki yadda ya kamata zai ci gaba da samun amincewa da hadin kai daga hukumar, yayin da duk wanda ya gaza ko ya karya jadawalin da aka amince da shi zai fuskanci hukunci bisa tanadin yarjejeniyar.

Ta kuma tabbatar da cewa muradun maniyyatan Najeriya su ne a gaba.

Sanarwar ta kara da cewa yarjejeniyar ta tanadi wa’adin gyara ga kamfanonin da suka samu tsaiko, da kuma daukar wasu matakai na daban idan ya zama dole domin kauce wa tangarda.

A nasa bangaren, Kwamishinan Ayyuka, Bincike da Ba da Lasisi na hukumar, Anofiu Elegushi, ya ce yarjejeniyar na nuna karfafa hadin kai da kuma kudurin samar da ingantaccen aiki.

Ya ce darussan da aka koya daga jigilar hajjin 2025 za su taimaka wajen inganta aikin shekarar 2026, yana mai cewa kiyaye lokaci, ingantaccen aiki, samar da isassun jirage da kuma tafiyar da kalubale yadda ya kamata su ne ginshikan nasara.

Da yake jawabi a madadin kamfanonin jiragen saman da ke cikin yarjejeniyar, Shehu Wada, babban darakta kuma wakilin Kamfanin Max Air, ya gode wa hukumar bisa amincewar da ta nuna musu.

Ya bayyana jigilar hajji a matsayin aiki na kasa baki daya, tare da tabbatar da kudurin kamfanonin wajen kiyaye tsaro, bin lokaci da kuma mutunta jadawalin da aka amince da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here