Gwamnan Kano ya karbi bakuncin tawagar bankin Duniya

Gwamnan, Kano, tawagar, bankin, Duniya
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin ya karbi bakuncin daraktan bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri da tawagarsa a fadar gwamnatin Kano...

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin ya karbi bakuncin daraktan bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri da tawagarsa a fadar gwamnatin Kano.

Yusuf ya bayyana hakan ne a shafin sa na X, ranar Talata.

Gwamnan ya yaba da shirye-shiryen Bankin Duniya a fannonin ilimi da kiwon lafiya, da kuma sauyin yanayi da sauran fannoni a Kano da kudu na ci gaba da tallafawa bankin.

Karin labari: Ruɗani a Majalisar Dattijan Najeriya kan zargin cushe a kasafin kuɗi

Da yake raba hotuna daga ziyarar, ya rubuta cewa, “Ina farin cikin karbar bakuncin Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mista Shubham Chaudhuri, tare da tawagarsa, a gidan gwamnati jiya.

“Na yi amfani da wannan dama wajen yaba wa Bankin Duniya bisa ayyukansu daban-daban a fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma sauyin yanayi da sauran fannoni a Kano.

Karin labari: Al-Qa’ida ta sanar da mutuwar shugabanta a Yemen

“Na kuma yi kira da a kara jajircewa daga bankin na jihar Kano, domin gwamnatin jihar a karkashina aminiya ce ga bankin da sauran abokan huldar ci gaba.

“Gaba ɗaya, mun kasance da haɗin kai sosai, kuma na gode wa Mista Chaudhuri da ƙungiyar WB saboda goyon bayan da suka bayar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here