Majalisar dokokin Kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma’aikata

Majalisar, Dokokin, Jihar, Kano, shugabannin, hukumar, rushe, daukar, ma'aikata
Majalisar dokokin jihar kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma'aikata na najalisar, sakamakon gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata...
Majalisar dokokin jihar kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma’aikata na majalisar, sakamakon gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Da yake gabatar da kudurin gaggawa domin amfanin al’umma kan bukatar rushe su, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ‘Yan Gurasa ya ce shugabannin hukumar ba sa zuwa wajen aiki.

Karin labari: Daliban jihar Kebbi da ke karatu a Indiya da Masar na fuskantar barazana

Haka zalika ba sa gudanar da ayyukan da aka dora musu yadda ya kamata bisa tsari da cancanta.
A zaman majalisar wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maye gurbin da wadanda suka cancanta bisa tanadin dokar hukumar sashe na 51.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here