NBA ta taya Awomolo murnar zama shugaban kungiyar Benchers

NBA, Chief, Adegboyega Awomolo, taya, murna, zama, shugaban, kungiyar, Benchers
Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Abuja ta taya babban Lauyan Najeriya (SAN), Cif Adegboyega Awomolo, murnar zama shugaban kungiyar Benchers na 52...

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Abuja ta taya babban Lauyan Najeriya (SAN), Cif Adegboyega Awomolo, murnar zama shugaban kungiyar Benchers na 52.

Shugaban reshen, Mista Afam Okeke ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin, inda ya ce NBA ta yi farin ciki da fitowar Awomolo a matsayin shugaban kungiyar benchers.

Karin labari: Majalisar dokokin Kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma’aikata

“Ba mu yi mamakin fitowar sa ba, duba da yadda ya sadaukar da kai ga aikin shari’a da kuma bil’adama.

“Shi ne shugaban NBA, reshen Ilorin a 1990 kuma shugaban kwamitin shugabanni da sakatarorin rassan NBA 44 a 1996 (Kwamitin da ya farfado da NBA bayan rikicin Port Harcourt na 1992),” in ji shi.

Karin labari: Daliban jihar Kebbi da ke karatu a Indiya da Masar na fuskantar barazana

Okeke ya ɗaukaka kyawawan halaye na Awomolo, yana kwatanta shi a matsayin jigon juriya kuma jakadan da ya cancanci reshe.

“Shi dattijo ne kuma jagora na gaskiya, kamar yadda shi ma abin koyi ne kuma mai ba da shawara ga masu bin doka da oda.

“Muna taya shi murna a yau, kamar yadda aka saba, muna yi masa fatan samun nasara a matsayin shugaban kungiyar masu daraja ta 52,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here