
Wani dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ondo, Paul Akintelure, ya rasu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun marigayin, Oladapo Akintelure, ya ce ya mutu ne da sanyin safiyar ranar Talata, kwanaki bayan da ya yi korafi kan zargin barazana ga rayuwarsa.
Za’a yi zaben gwamnan Ondo a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Karin labari: Majalisar Togo ta amince da kundin tsarin mulkin kasar da ta yiwa kwaskwarima
Rahotanni sun bayyana cewa mai fatan kujerar gwamnan ya koka da ciwon kirji sa’o’i kadan kafin rasuwarsa.
Akintelure, wanda likita ne, ya fito ne daga Igbotako, karamar hukumar Okitipupa ta Ondo.
A ranar alhamis din da ta gabata, ya daga murya kan barazanar da ake zargin sa da yi wa rayuwarsa.
Karin labari: Kotu Ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
“Da farko, ina fatan wadannan al’amura za su watse cikin lokaci, amma abin takaici, sun kara yin barazana ga rayuwata,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
“Barazanar da ake yi min ne ya ƙarfafa na tsaya tsayin daka don tabbatar da gaskiya da adalci. Ba zan bari tsoro ya sa mu gaba ba.
“Mu rungumi zaman lafiya da ci gaba da kuma hadin kai. Ƙarfin haɗin gwiwarmu ya ta’allaka ne a cikinmu, mu tsaya tare a matsayi ɗaya, ba tare da la’akari da bambancinmu ba.












































