Gobara ta lalata motoci 8 da rumfuna a jihar Kano

Gobara, lalata, motoci, rumfuna, jihar, kano
Wata gobara ta lalata motoci kusan takwas da rumfuna da kayan aikin kafinta ranar Talata a Kano. Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe...

 

Wata gobara ta lalata motoci kusan takwas da rumfuna da kayan aikin kafinta ranar Talata a Kano.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a wani gini da bai kammala ba da ake amfani da shi wajen aikin kafinta da gyaran mota, da ke hanyar Lawan Dambazau ta hanyar jirgin kasa a jihar Kano.

Karin labari: Gwamna Yusuf Ya Nada Dan Kwankwaso Da Wasu Mutane 3 A Matsayin Kwamishinoni

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun isa wurin da lamarin ya faru bayan kiran gaggawa da jami’in ‘yan sanda na Kwalli ya kai dakin kula da hukumar, inji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gobara ta kama ne ciki har da rumfuna takwas dauke da kayan aikin kafinta da kuma motoci takwas da suka kone, sai dai an san samu rumfa daya da mota daya da lamarin bai shafa ba.”

Karin labari: Kotu Ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

“Da taimakon Allah da kuma kokarin mutanenmu, mun yi nasarar ceto kusan rumfuna 10 da masallacin wucin gadi guda 37 kuma an ajiye motoci 37 a garejin.”

Gobara 2

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here