Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gurfanar da wani alkali na kotun majistare mai suna Muhammad Suleiman Kumo a gaban mai shari’a H. H. Kereng na babbar kotun Gombe bisa zargin karɓar rashawa da tursasawa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an gurfanar da Kumo ne bisa tuhuma uku da hukumar EFCC shiyyar Gombe ta shigar dangane da abin da ya shafi karɓar kuɗaɗe daga wani ma’aikacin rajistara da yake aiki a kotun da yake jagoranta.
Rahoton ya bayyana cewa an samu alkalin da karɓar kuɗi Naira Miliyan Daya ta hanyar asusun bankin Zenith mai lamba 2273938871 da ke da alaƙa da wani Adamu Ahmad wanda ke matsayin rajistara a kotun, lamarin da ya saba da tanadin dokar yaƙi da cin hanci da rashawa ta shekarar 2000.
Haka kuma a wata tuhuma cewa a cikin watan Nuwamba shekarar 2024 an sake zargin alkalin da karɓar kuɗi dubu Ɗari huɗudaga wannan rajista ta wannan asusun, abin da doka ke ɗauka a matsayin laifi mai tsanani.
Wanda ake tuhuma ya musanta laifukan gaba ɗaya, abin da ya sa lauyan gwamnati ya nemi kotu ta tura shi gidan gyaran hali tare da ɗaura ranar fara shari’a, sai dai lauyansa ya nemi a ba shi beli wanda bangaren gwamnati ya ƙi amincewa da shi bisa hujjar doka.
Mai shari’a Kereng bayan sauraron bangarorin biyu ya bayar da belin wucin gadi ga wanda ake tuhuma, yana mai cewa alkalin ya samu belin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa tun farko kuma ya bayyana kansa ga kotu ba tare da wata matsala ba.
Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 13 da 14 ga watan Janairu shekarar 2026 domin yanke hukunci kan batun belin tare da ci gaba da sauraron ƙarar da ake yi masa.










































