Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta tabbatar wa da kwangila na ayyukan gine-ginen hanyoyi cewa za ta biya duk kuɗaɗen da suke bi kafin ranar 20 ga Disamba, 2025 bayan makonni na zanga-zangar da suka yi kan jinkirin biyan bashin da ya janyo tsaikon aiwatar da ayyuka.
Ministan ayyuka David Umahi ya bayyana hakan yayin bude gadar Keffi da aka gyara a jihar Nasarawa, inda ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa kwamiti na musamman domin tantance dukkan bashi tare da tabbatar da biyan su.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa yan kwangilar da suke aikin hanyoyin tarayya sun yi zanga-zanga a ma’aikatar kudi saboda jinkirin biyan kuɗin da suka kashe, ciki har da na shekarar 2024.
Kungiyar yan kwangilar Arewa na Gida ta Najeriya ta bayyana cewa tana bin gwamnati kusan Tiriliyan Huɗu, tare da neman a saki Biliyan Ɗari Bakwai da Sittin da aka yi alkawarin biya tun watan Satumba.
Karanta: EFCC ta gurfanar da wani alkali kan zargin rashawa
Masu zanga-zangar sun kai guntun akwatin jana’iza a kofar ma’aikatar kudi a matsayin alamar wahalar da suka sha saboda kin biyan su.
Ministan ayyuka ya ce ba bu bukatar ci gaba da zanga-zanga saboda shugaban kasa ya umurci a biya dukkan basussukan da aka tantance.
Ya ce akwai kamfanoni da dama da ba su samu an biya su kudin aikin Maraba–Keffi, ciki har da kamfanin gine-gine na China Harbour, amma za su samu a cikin sabon tsarin biyan kuɗaɗen.
Umahi ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta gayyaci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC da kuma hukumar EFCC domin duba dukkan ayyukan hanyoyin tarayya da ake yi ko aka kammala a fadin jihohi da babban birnin tarayya, da nufin tabbatar da gaskiya da ganin cewa kuɗin da ake biya ya dace da aikin da aka yi.
A cewarsa, gwamnati na shirin kaddamar da sabon tsarin internet domin a rika bibiyar ci gaban ayyuka a zahiri.
Yayin bude gadar Keffi da ta rushe a watan Yuli, Umahi ya ce shugaban kasa ya bayar da kuɗin gyaran cikin awanni ashirin da huɗu, lamarin da ya kira abin mamaki.
Ministan ya kare tsarin aikin hanyar Abuja–Kano inda ya ce canje-canjen da aka yi a tsare-tsaren aikin sun sa jinkiri amma an kammala fiye da kilomita arba’in da huɗu na titin.













































