Magidanci dan shekara 60, Malam Bala tare dan sa Sunusi Bala, mai shekaru 33 sun wada wata tsohowar rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a karamar hukumar Wudil, da ke cikin jihar Kano, inda suka rasa rayukansu kafin a kai ga cetosu.
Maimagana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da mutuwar ta su, yau laraba a Kano, inda ya ce uba da dan nasa sun rasu ne ya yin da suke ibar ruwa a rijiyar.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da safe.
“mun sami kiran gaggawa daga ofishin hukumar kashe gobara na Wudil, da misalin karfe 11: 30 na safe, cewa uba da dan sa sun wada rijiya”
“Nan take muka tura jami’an mu domin cetosu”
Sanarwar ta tabbatar da cewa an sami nasarar fito dasu daga rijiyar, amma jim kadan bayan fito da su, suka ce ga garin kun nan.











































