Gwamnan Kano ya tallafawa Alhazai 2,906 kowannen su da Naira 500,000

NAHCON, gwamna, kano, Abba, tallafawa, alhazai
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin Naira dubu dari biyar 500,000 ga maniyyata 2,906 da suka biya kudin aikin Hajjin bana a...

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin Naira dubu dari biyar 500,000 ga maniyyata 2,906 da suka biya kudin aikin Hajjin bana a karkashin kulawar hukumar jindadin alhazai ta jihar Kano.

SOLACEBASE ta bayyana cewa an baiwa jihar Kano kujeru 5,934 da hukumar alhazai ta kasa ta ware domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024.

Sai dai kawo yanzu maniyyata 2,906 ne kawai suka biya kudin ajiya kafin hukumar NAHCON ta sanar da karin kudin shiga na Naira Miliyan 1.9.

Karin labari: BDC sun karyata sayar da Dala daga 900 zuwa Naira 1,000

Darakta Janar na Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Dan Bappa, ya sanar da tallafin da gwamnatin jihar ke baiwa alhazai a wata ganawa da manema labarai a Kano ranar Laraba.

“A bisa la’akari da karin kusan Naira miliyan daya da dubu dari tara da goma sha takwas da hukumar alhazai ta Najeriya ta yi a kan kowace kujerar aikin Hajji, ina mai farin cikin sanar da daukacin mazauna jihar Kano cewa gwamnatin jihar ta yi ragi na dari biyar, wato Naira dubu (₦500,000) ga kowace kujera,” in ji shi.

Karin labari: “Zamfara a yanzu ita ce babbar wajen ta’addanci” – Gwamna Lawal

“Wannan yana nufin a maimakon biyan karin Naira miliyan daya da dubu dari tara, mahajjaci zai biya kusan Naira dubu dari hudu da goma sha takwas. Wannan tallafin zai shafi wadanda suka rigaya sun biya kuma suka karbi rasit daga gare mu. Wadanda har yanzu ba su biya kudinsu ba, za’a bukaci su biya daidai adadin kamar yadda hukumar alhazai ta kasa ta sanar.”

“Gwamnan jihar Kano ya yanke wannan shawarar ne domin rage wa maniyyatan da ke da niyyar biyan sauran kudaden aikin Hajji, kamar yadda NAHCON ta umarta.”

Karin labari: Gobara ta lalata motoci 8 da rumfuna a jihar Kano

“Jimlar kudaden da gwamna ya biya na maniyyata mahajjata dubu biyu da dari tara da shida 2,906 sun kai naira biliyan daya da miliyan dari hudu da hamsin da hudu.”

Babban Daraktan ya ci gaba da cewa, wadanda za su ci gajiyar tallafin aikin Hajji su ne wadanda suka rigaya sun biya kudin wani kaso ga hukumar, inda ya ce sama da maniyyata 2,906 sun riga sun biya nasu kudin da hukumar ta biya.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya sake sabon nadi

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin in nuna godiyata ga mai girma, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa wannan karamcin. Hakika ya cancanci a yaba masa,”

“Ina so in tunatar da dukkan maniyyata cewa wa’adin biyan sauran ma’auni shi ne gobe. Da fatan za’a tabbatar cewa kun kammala biyan kuɗi kafin ranar ƙarshe. Hukumar Alhazai ta Najeriya ba ta kara wa’adin ba, don haka gobe ya rage ranar ƙarshe don biyan kuɗi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here