Kotu ta bada umarnin a kwace Naira Biliyan 1.1 na wucin gadi da ake zargin suna da alaka da gwamnatin Kano

Gov. Yusuf and Abdullahi Rogo 3 750x430

Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kwace sama da Naira Biliyan 1.1  na wucin gadi da ake zargin an fitar da su ba bisa ka’ida ba daga asusun rabon kudaden tarayya na Jihar Kano da ke ajiye a bankin United Bank for Africa.

Alkalin kotun, Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ne bayan lauyan hukumar ICPC ya gabatar da bukata ta gaggawa, inda kotun ta tabbatar da cewa bukatar ta cancanta tare da amincewa da ita.

Kotun ta kuma bayar da umarnin a wallafa wannan umarnin kwacewar a wata jarida ta kasa domin duk wanda ke da sha’awa ko ikirari a kan kudaden ya fito ya bayyana dalilin da ya sa ba za a mayar da kudaden mallakin gwamnatin tarayya ba.

Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci domin duba matakin bin umarnin da kotun ta bayar.

A cikin karar da aka shigar a kotu, an bayyana sunan gwamnatin Tarayya tare da kudin Naira 1,109,230,000 da ke ajiye a asusun dawo da kadarori na hukumar ICPC.

Takardun shari’ar sun nuna cewa an shigar da karar ne bayan bincike kan wani koke da aka samu daga wasu ‘yan Jihar Kano dangane da fitar da kudade daga asusun rabon kudaden tarayya na jihar domin abubuwan da ba su da alaka da harkokin gwamnati.

Hukumar ta nemi kotu ta bayar da umarnin kwace kudaden na wucin gadi, tana mai bayanin cewa an gano kudaden ne a yayin bincike kuma ana zargin su a matsayin ribar ayyukan da ba su dace da doka ba.

Karanta: Zargin cin hanci: ICPC ta gayyaci Aliko Dangote kan ƙorafin da ya shigar na tsohon shugaban NMDPRA

Har ila yau, an nemi kotun ta umarci a sanar da jama’a domin duk mai ikirari ya samu damar gabatar da hujja kafin yanke hukunci na karshe.

A cikin rantsuwar da aka gabatar, wani jami’in yaki da cin hanci ya bayyana cewa bincike ya nuna an ba da izinin biyan kudin ne ga wasu kamfanonin canjin kudi bayan gabatar da takardun izini daga wasu kamfanonin mai da iskar gas.

Binciken ya kuma nuna cewa wadannan kamfanoni sun amsa cewa babu wata kwangila ta gaske da aka aiwatar, kuma ba a samar da dizal ko wasu kayayyaki ga gwamnatin jihar ba.

Haka kuma, binciken ya gano cewa an mayar da wadannan kudade zuwa dalar Amurka tare da mika su ga wani jami’in gwamnatin jihar a ofishin hulda na jihar da ke Abuja.

Wannan jami’i ya amince da karbar kudin a rubuce yayin da hukumar ke ci gaba da bincike, lamarin da ya sa aka samu nasarar dawo da mafi yawan kudaden daga cikin adadin da aka fitar.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa bayar da umarnin kwacewa na wucin gadi zai taimaka wajen kare kudaden har sai an kammala sanar da jama’a da kuma yanke hukunci na karshe.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here