Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) ya nada Suhaib Auwal Gwagwarwa a matsayin kakakin yakin neman zaben sa.
Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan takarar jam’iyyar PRP ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Sanarwar ta ce Mista Suhaib, kwararren dan jarida ne mai dimbin gogewa a harkokin talabijin, rediyo, aikin jarida na Internet da kuma kafofin sada zumunta.
”Mr. Suhaib ya fara aikin jarida ne a gidan rediyon Freedom Kano, kuma ya samu rike matsayin mai dakko rahotanni kuma mai kula da kafafen labarai na zamani. Ya yi aiki a Liberty TV, Kaduna.
Ya kuma yi aiki da wasu kafafen yada labarai na Internet a Kano, wadanda suka hadar da Jaridar SOLACEBASE da Daily News 24.
Kafin nadin nasa, Suhaib yana aiki a ofishin Gaskia TV Ghana dake Kano a matsayin mataimakin shugaban ofishin Kano, da kuma Premier Radio a matsayin mai ba da shawara kan kafofin watsa labarai na zamani.
Sabon Kakakin Yakin Neman Zaben Gwamna na PRP ya samu digiri na biyu a fannin aikin Jarida daga Jami’ar Igbinedion Okada da ke Jihar Edo, kuma ya halarci kwasa-kwasai da karatuttuka da dama a ciki da wajen Najeriya.