Gobara ta lalata kadarori na Miliyoyin Naira a kasuwar Singa ta Kano

WhatsApp Image 2026 02 02 at 09.34.25 750x430

Wata gobara ta lalata manyan shaguna uku a shahararriyar kasuwar nan ta Singa da ke cikin birnin Kano, lamarin da ya jawo asarar kaya da dukiyoyi masu darajar Miliyoyin Naira.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Litinin, inda ta shafi tubalan kasuwa biyu da aka fi sani da Gidan Mazaf da Gidan Mangaro.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe ɗaya na dare, inda ta bazu cikin gaggawa ta cinye manyan shaguna uku kafin daga bisani aka samu damar shawo kanta.

Shugaban Gidan Mangaro, Alhaji Abba Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Solacebase, inda ya bayyana cewa an sanar da shi game da gobarar ne da misalin ƙarfe huɗu na asuba, kuma ya tarar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun riga sun isa wurin suna aiki.

Karanta: Zaria: Fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh “Rigi-Rigi” Kusfa ya rasu yana da shekara 57

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tare da taimakon kamfanonin Aspire da Mamuda sun yi gaggawar shiga aikin kashe gobarar, lamarin da ya taimaka wajen hana ta bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar, duk da haka wani daga cikin shagunan da gobarar ta shafa ya ƙunshi kayayyakin da darajarsu ta kai kusan Naira Miliyan Talatin waɗanda suka ƙone gaba ɗaya.

Shaidu sun bayyana cewa an tura motocin kashe gobara da dama zuwa wurin, yayin da wasu kamfanoni masu zaman kansu suka bayar da tankokin ruwa don tallafawa aikin.

Tuni dai jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin gobarar da kuma tantance adadin shagunan da abin ya shafa da jimillar asarar da aka yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here