Gwamnatin tarayya ta fara biyan cikon Naira 44,000 tsofaffin ‘yan hidimar ƙasa NYSC.
Fara biyan kudin wani ɓangare ne na cika alkawarin da aka yi a baya wanda ya danganci karin alawus din matasan na wata-wata daga Naira 33,000 zuwa Naira 77,000.
Biyan dai ya shafi wadanda suka kammala hidimar ƙasar kafin sabon alawus din ya fara aiki a farkon wannan shekarar.
Wasu tsofaffin ‘yan hidimar kasa ne suka bayyana fara biyan kudin shafin X watau a baya inda suka tabbatar da karbar kudin, suna nuna godiya da jin dadinsu.
Biyan, wanda ake kallo a matsayin cika alkawarin da gwamnati ta yi a baya, ya jawo hankulan jama’a a kafar Internet inda da dama ke yabawa.
NAN













































