Wasu fusatattun daliban kwalejin kimiyya da fasaha da ke Jega a jihar Kebbi sun banka wa gidan shugaban kwalejin Haruna Saidu-Sauwa wuta tare da lalata motar sa.
Zanga-zangar ta samo asali ne bisa zargin sa da almundahanar Naira miliyan 23 da aka karba daga hannun dalibain kwalejin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa za a yi karin bayani da zarar an samu bayanai daga jami’in ‘yan sanda na Jega.