An shawarci masu ababen hawa da ke bin babbar hanyar Bida zuwa Minna a jihar Neja da su yi hattara agarin Sabon-Gida da ke karamar hukumar Gbako sakamakon rugujewar wata gada a Gbako.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa a jihar Mista Habibu Egigogo ne ya yi wannan gargadin lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya.
“Akwai wata gada da ta ruguje a Sabon-Gida da ke kan hanyar Bida zuwa Minna; Muna shawartar masu ababen hawa da su yi taka tsantsan lokacin da suka zo saitin gurin.
“An samar da wata hanyar ratse ta dabam ga kananan motoci, yayin da jami’an hukumar dake Bida ke wurin dan kula tareda sa ido ga ababen hawan” inji shi.
Egigogo ya ce gadar ta ruguje ne a ranar Lahadin da ta gabata sakamakon matsin lambar da manyan motocin daukar dakon kaya suka yi mata.
“Gwamnati ta hana manyan ababen hawa bin hanyar, amma se cikin dare kullum su ke biyo hanyar,” inji shi.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya ya rawaito cewa a lokacin da lamarin ya wakana, an samu cinkoso a kan titin, wanda hakan ya sanya masu ababen hawa da matafiya daukan dogon lokaci kafin warware matsalar.
Malam Aliyu Mohammed, wani direban ‘yan kasuwa ne ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Najeriya cewa, sai da masu ababen hawa suka koma Gbako ta hanyar Zungeru zuwa Minna, wanda ya 6ille ta hanyar Bida zuwa Minna kamar yadda aka saba.












































