A ranar juma’a hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda ya kasance mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ma’aikata a zaben 2023 tare da Peter Obi, domin yi masa tambayoyi kan wasu kalaman da ake ganin na iya haddasa tarzoma ga ƙasar.
A cewar wata majiya ta tsaro, Baba-Ahmed wanda kuma shi ne wanda ya kafa jami’ar Baze, an gayyace shi ne bisa zargin ci gaba da fadin kalaman da ake ɗauka masu tayar da hankalin jama’a, musamman a yanayin siyasar Najeriya ta yanzu.
Majiyoyi sun bayyana cewa hukumar tana bibiyar kalamansa a kafafen yada labarai, musamman dangane da ikirarin da ya sha yi cewa ƙasar na fuskantar “rikicin tsarin mulki,” tare da zargin kotu da rundunar soji da gazawa wajen dakatar da rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.
Ko a kwanakin baya ya bayyana a talabijin inda ya dora alhakin rantsar da gwamnatin Tinubu kan abin da ya kira gazawar kotu da soji, har ma ya yi kalaman da ake hange suna iya tunzura jami’an tsaro, lamarin da ya kara jawo hankalin hukumomi.
Majiyar ta ce hukumar tsaron DSS na ganin irin wadannan kalamai na iya kara dagula yanayin siyasa, musamman ganin yadda irin wadannan maganganu suka haifar da rashin kwanciyar hankali a kasashe kamar Guinea-Bissau da wasu kasashen yammacin Afirka.
DSS ta ce gayyatar da aka yi masa ba hukunci ba ne, amma matakin rigakafi ne domin fayyace manufarsa, da takaita duk wani abu da zai iya rikita jama’a ko raunana amincewar su ga hukumomin gwamnati, musamman ganin cewa ya taba bayyana kokarin inganta tsaro a matsayin abin dariya.
Hukumar tsaro ta DSS ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba tukuna.













































