Trump ya maka gidan talabijin na CNN kotu

FB IMG 16648828707338332
FB IMG 16648828707338332

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya maka gidan Talabijin na CNN kotu bisa zargin bata masa suna.

Trump ya zargi sanannen gidan talabijin din na Amurka da bata masa suna, inda yace sun kwatanta shi da Adolf Hitler na Jamus.

Akan haka tsohon Shugaban Amurkar ya nemi diyyar dala miliyan ɗari huɗu da saba’in da biyar.

Donald Trump ya shigar da kara mai shafi 29 a wata kotu da ke Florida, inda yake zargin CNN da ƙoƙarin yi masa maƙarƙashiya.

To amma zuwa yanzu gidan talabijin na CNN din bai mayar da martani ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here