Yan bindiga sun kashe amarya da ango a karamar hukumar Riyom dake cikin jihar Plateau.
Amaryar da ango duk malaman makarantar BECO Comprehensive High dake jihar, ya yin kai harin an jikkata mataimakin shugaban makarantar a ranar Litinin.
Harin ya faru ne ya yin da malaman makarantar ta BECO Comprehensive High school suke tsaka da gudanar da aikin su a makarantar.
Kakin rundunar da yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.
Sai dai kuma bai yi cikakaken bayani ba, amma yace suna bincike akan faruwar lamarin.













































