Bayan shafe shekaru 20 a majalisa, kakakin majalisar Yobe ya sha kaye ga matashi Dan shekara 29

IMG 20230319 WA0065
IMG 20230319 WA0065

Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe Hon. Ahmed Lawan Mirwa na jam’iyyar APC mai mulki ya rasa kujerarsa a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka kammala, Asabar, Maris.

Lawan Mirwa wanda ke wakiltar mazabar jihar Nguru a majalisar dokokin jihar Yobe tun a shekarar 2003, ya sha kaye a hannun matashin dan takarar jam’iyyar PDP Musa Lawan Majakura.

Jaridar Solace base ta rawaito cewa Musa Lawan Majakura na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 6,648, inda ya doke Ahmed Lawan Mirwa na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 6,466.

Bukar Jatau na NNPP ya samu kuri’u 23, yayin da Mai Zare Idriss Idriss na APM ya samu kuri’u 14 sai Isah Sa’idu Shehu na jam’iyyar ADC ya samu kuri’u 30.

Wannan shi ne sakamakon zaben, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, jami’in zabe na jihar Nguru, Alhaji Mahdi Damatu ya bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here