Tsohon mai horar da kungiyar Super Eagles Christian Chukwu ya rasu yana da shekaru 74

Christian Chukwu

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Rangers International FC a jihar Enugu da akafi sani da “Chairman”, wato Christian Chukwu, ya rasu.

Chukwu, dake tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa ’ Green Eagles, ya rasu yau Asabar a jihar ta Enugu yana da shekaru 74.

Joe Martins Uzodike, tsohon sakataren kungiyar kwallon kafa ta Rangers International ne ya sanar da rasuwar tasa ga kamfanin Dillancin Labarai na NAN a yau Asabar.

An haifi Chukwu, a ranar 4, ga watan Janairun shekarar 1951, kuma shi yasanyawa kungiyar kwallon kafa ta kasa Green Eagles, kyaftin a tsakanin shekarun 1974 zuwa 1980.

Yana daga cikin tawagar kasar nan da ta lashe gasar cin kofin Afrika a shekarar 1980 kuma yana daya daga cikin kyaftin din Najeriya da yaja ragamar kasar nan wajen lashe gasar da ci 3-0 a kan kasar Algeriya a wasan karshe a shekarar.

A watan Oktobar shekarar 1998, kasar Kenya ta nada shi a matsayin sabon kyaftin din yan wasan kasar ta, sannan a shekarar 2003 zuwa 2005 ya rike yan wasan Najeriya a matsayin mai horarwar su.

A shekarar 2006 a Chukwu ya samu matsin lamba sakamakon rashin nasarar cin wasanni biyu da ya yiwa Najeriya na neman Tikitin buga gasar cin kofin Duniya wanda hakan yasa aka dakatar da shi.

Chukwu ya rike ragamar horar da yan wasan kungiyar Rangers a shekarar 2008/2009 wanda ya kaisu matakin na 6 a gasar Premier ta Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here