Yanzu-Yanzu: Gwamna Yusuf ya rantsar da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna

IMG 20260505 WA0226

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Hon. Murtala Sule Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamna, a wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Babbar Alkaliyar jihar, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ce ta jagoranci rantsuwar a gaban manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisa, sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Daga cikin manyan baki da suka halarci wurin akwai tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da sauransu.

Cikakken bayani nan ba da jimawa ba…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here