Shugaban Jami’ar MAAUN ya yi alhinin rasuwar fitaccen dan jarida Saleh Ashaka

IMG 20260504 WA0012 2026 05 04 118

Shugaban Rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar tsohon wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) kuma fitaccen dan jarida, Saleh Shehu Ashaka, a matsayin babban rashi ba ga aikin jarida kadai ba, har ma ga kasa baki daya.

Jaridar SolaceBase ta tuna cewa Saleh Shehu Ashaka ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa marigayi Ashaka ya rayu rayuwa mai tasiri da hidima, inda ya sadaukar da aikinsa wajen kare da’a da kwarewar aikin jarida. Ya kuma bayyana shi a matsayin dan jarida jajirtacce wanda aikinsa ya ba shi daraja a fadin kasa da ma waje.

“Saleh ba fitaccen dan jarida ba ne kawai, mai taimakon jama’a ne wanda ya taba rayuwar mutane da dama. Karamcinsa ga abokan aiki da kuma yawaitar sakonnin ta’aziyya a fadin kasa ya nuna irin halinsa na kwarai, mai tawali’u, kuma mai alheri,” in ji shi.

Ya kuma cewa Ashaka na daya daga cikin fitattun wakilan da VOA ta tbɓa samarwa, wanda aka so saboda natsuwa, muryarsa mai sanyaya zuciya da kuma salon rahotonsa na daidaito, wanda ya sanya shi kaunatacce ga masu sauraro tsawon shekaru.

Gwarzo ya kara da cewa rasuwar marigayin ta bar wani gibi da zai yi wuya a cike, musamman a wannan lokaci da aikin jarida ke bukatar muryoyi masu gogewa da ka’ida.

Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyali, abokai, da abokan aikin marigayin, yana addu’a ga Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuransa, ya ba shi Aljannatul Firdaus, kuma ya ba wadanda ya bari juriyar jure rashin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here