
Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano ta ce za ta fara jigilar maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 a ranar 14 ga Mayu.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar wa manema labarai a ranar Litinin a Kano.
Dederi ya bayyana cewa Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim-Matawalle ya bayyana hakan a wurin bikin rufe bita ga maniyyata aikin Hajji da aka gudanar a Makarantar Nazarin Larabci dake Kano.
A cewar Daraktan, ranar ta yi daidai da jadawalin da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta fitar.
“An zabi kamfanin Max Air a matsayin jirgin da zai yi jigilar maniyyatan jihar a hukumance.
Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali,” in ji shi.
Tun da fari dai, Shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Lawan, ya bukaci maniyyatan da su rika karanta littattafan da aka ba su na nuna yadda ake aikin Hajji akai-akai don karin fahimtar ayyukan Hajji.
Ya kuma shawarce su da su bi ka’idoji da dokokin hukumomin Najeriya da na Saudiyya sosai a duk tsawon aikin Hajjin. (NAN)










































