Ɗalibai mata da aka sace a Zamfara sun shaƙi iskar ƴanci

zamfara 306x165 1
zamfara 306x165 1

Huɗu daga cikin ɗalibai mata da aka sace su na Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Zamfara sun shaƙi iskar ƴanci.

Mataimakin shugaban kwalejin Jamilu Lawali, ne ya tabbatar da sakin nasu ga gidan talabijin na Channels ta hanyar tattaunawar su ta wayar tarho da yammacin Alhamis ɗin makon nan.

A cewarsa, waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban sun sako mata huɗu daga ciki ranar Alhamis a wani wuri da ke kusa da garin Tsafe.

Haka kuma ya ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin sarkin nasu.

“An sake su da yammacin yau a wani wuri kusa da garin Tsafe, makarantar ba ta biya ko kwabo ba domin a sake su,” inji shi.

Daliban hudu a halin yanzu suna wani asibiti da ba a bayyana ba suna karɓar kulawar jami’an lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here