‘Ƴan bindiga sun kashe mutum 12 da ƙona gidaje a jihar Neja

'Yan bindiga, kashe, mutane, gidaje, neja, Hon. Akiku Kuta
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja na cewa wasu da ake zargin mayaƙan kungiyar Boko Haram ne sun kashe sama da mutum goma sha biyu tare da...

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja na cewa wasu da ake zargin mayaƙan kungiyar Boko Haram ne sun kashe sama da mutum goma sha biyu tare da ƙona kimanin gidaje talatin a wasu jerin hare-hare da suka kai.

Mazauna yankunan sun ce hare-haren sun faru ne a tsawon makon da ya gabata, a garuruwan Alawa da Bangajiya da sauran su, inda baya ga kashe mutane da dama da maharan suka yi sun kuma yi awon gaba da dukiya mai ɗimbin yawa.

Karanta wannan: Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta haramta safarar fatar jaki

Wani Mazaunin garin ya tabbatar da cewa sama da makonni biyu ke nan suke fama da tashe-tashen hankula na hare-haren ‘ƴan bindiga waɗanda suka hana su sukuni.

A cewar sa, a makon da ya gabata ne ƴan bindigar suka dasa bam a hanya wanda ya tashi da wasu da ke kan hanyar komawa ƙauyukansu daga kasuwa kuma nan take mutane aƙalla 8 suka rasa rayukansu.

Karanta wannan: “Babu sakamako a binciken mutuwar Navalny” – Kremlin

Da aka je kwashe gawawwakin waɗanda aka kashe kuma aka sake kai wani harin da ya yi sanadiyar asarar rayuka sannan suka hana daukar gawawwakin wanda har ya zuwa yanzu babu labarin kwashe gawawwakin.

Shugaban ƙaramar Hukumar Shiroro Hon. Akiku Kuta ya tabbatar da harin

Wadannan sabbin hare-haren dai sun sa mutane da dama yin hijira zuwa wasu makwabtan garuruwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here