Majalisar dattijai a ranar Laraba ta cire dokar da ta tilasta zaben fidda gwani na ‘yan takara a jam’iyyun siyasa kai tsaye daga dokar zabe da aka gyara.
Yanzu haka dai ta yi gyaran fuska kan sadara ta 84, inda ta ba da damar gudanar da zabukan kai tsaye, da wand aba kai tsaye ba, da kuma yin sulhu wajen fitar da ‘yan takarar jam’iyyun siyasa.
Idan dai za a iya tunawa, a karshen shekarar 2021 ne Majalisar Dattawa ta zartar da kudirin dokar tare da mika wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ki amincewa da kudirin gyaran dokar zabe.
Shugaba Buhari ya ce yin amfani da zaben fidda gwani na kai tsaye ga dukkan jam’iyyun siyasar kasar zai yi tsada da yawa wajen aiwatar da shi, yana mai cewa hakan zai jawo wani nau’in kasha kudi.
Ya kuma bayyana fargabar cewa shirin tilasta yin amfani da zabukan fidda gwanin kai tsaye zai kai ga tauye hakkin ‘yan kasa kuma zai kai ga mayar da kananan jam’iyyun siyasa saniyar ware.
Sashe na 84 (4) ya ci gaba da cewa, “Jam’iyyar siyasa da ta amince da tsarin zaben fidda gwani wanda ba kai tsaye ba domin zaben dan takararta, za ta bi tsarin da aka zayyana a kasa; (a) Dangane da batun fitar da dan takarar shugaban kasa, jam’iyyar siyasa za ta gudanar da babban taro na musamman a kowace jiha daga cikin jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja, inda wakilai za su kada kuri’a ga kowane mai neman tsayawa takara a wuraren da aka kebe a kowace Jaha a kan takamaiman ranakun.”
Sadarar ta tanadi cewa za a gudanar da babban taron kasa don amincewa da dan takarar da ya fi yawan kuri’u.
Gyaran dokar ya biyo bayan kudirin sake mika shi ga kwamitin na kasa baki daya.
Shugaban masu rinjaye, Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa) ne ya gabatar da kudiri a gaban majalisar.











































