Biyo bayan zama na musamman da aka yi tsakanin shugabancin kungiyar matuka baburan Adaidaita da hukumar KAROTA wanda kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano ta shirya, an cimma matsaya kan matsalolin da suka janyo kungiyar ta shiga yajin aiki.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugaban Hukumar KAROTA kan kafafen yada labarai na zamani Ayuba Jarimi ya aikowa Solacebase, ya bayyana cewa an amince ko wanne mai Babur din Adaidaita Sahu zai sabunta shaidar sa (wato Permit) akan kudi Naira 5,000, maimakon Naira 8,000 daga 19 ga watan Janairu 2022 zuwa ranar 28 ga watan Faburairu 2022. Duk wanda ya wuce Wannan rana bai sabunta ba, to zai biya Naira 8,000, maimakon Naira 5,000.
Haka kuma Zaman ya amince da biyan Naira 12,000 ga duk wanda zai yi sabuwar rijista, maimakon Naira 18,000 da aka saba biya. Shima dai daya yanzu zuwa ranar 28 ga watan Faburairu, Idan mutum ya wuce Wannan lokacin bai yi ba, zai biya Naira 18,000 maimakon Naira 12,000.
Sannan Zaman ya Amince a ci gaba da karbar Naira 100 a ko wace rana a matsayin harajin gwamnati, tare da biyan Naira 20 a matsayin kudin kungiya.
Duka bangarorin sun amince a ci gaba da karbar kudin har ranar lahadi, maimakon Ranar Litinin da ake biya Naira 200. Wannan tsari zai fara aiki ne sati na sama.
Zaman ya samu halartar bangaren gwamnati wanda shugaban Hukumar KAROTA Dakta. Baffa Babba Dan’agundi yake wakilta sai bangaren Kungiyar ‘yan Adaidaita Sahu karkashin Jagorancin Alh. Mansur Tanimu da kuma lauyan ‘yan Adaidaita Sahu Barrister Abba Hikima Fagge, sai Kuma Shugabancin kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano













































