Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya mayar da martani kan zargin da ake yiwa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai na shirin bata masa suna saboda burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2031.
SolaceBase ta ruwaito cewa El-Rufai a wata hira da yayi da Arise TV a ranar Litinin, ya yi zargin cewa Ribadu yana hada kai da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka masu zaman kansu domin lalata masa suna.
“Wani yana so ya lalata min suna. Me yasa? Nuhu Ribadu yana son ya zama shugaban kasa a 2031. Dole ne ya kawar da duk wani dan Arewa da yake ganin yana kan turbar.”
Sai dai Ribadu ya ce ‘’ in da shiru na ba zai sa a ce na yarda ba, da na yi watsi da shi. Ni dai na shagaltu da aikina na yanzu, don in yi fada da Nasir El-Rufai ko kuma wani a kafafen yada labarai ba ni da wannan lokacin “.