Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado

Muhuyi Magaji sabo

Kotun da’ar ma’aikata (CCT) a ranar Alhamis ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban kuliya bisa zargin saba ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, da cin hanci da rashawa, cin zarafin mukami, bayyana kadarorin karya, cin hanci da karbar kyaututtuka da dai sauransu.

Kotun ta amince da bukatar mai shigar da kara inda ta umurci wanda ake kara da ya a jiye mukamin sa na Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano bisa zargin saba wa tanadin kundin da’ar ma’aikata.

Kotun ta umar ci gwamnan Jihar Kano da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da su dauki dukkan matakan da suka dace wajen nada jami’in da ya fi dacewa da zai karbi ragamar shugabancin Hukumar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here