An ba da umarnin rubanya yawan jami’an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna

police 750x430
police 750x430

Babban Sifeton ‘yan sandan kasa Kayode Adeolu Egbetokun ya bada umarnin kara yawan jami’an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Wannan dai wani mataki ne na tsaurara matakan tsaro domin inganta zaman lafiya a kan titin.

Karanta wannan: Jami’ar Don ta gargadi Mata da su kaucewa shan miyagun kwayoyi

Da yake bayyana muhimmancin samar da tsaro domin zirga-zirga a yankin, babban sifeton ‘yan sandan ya ce za a kara girke jami’an ‘yan sanda da kayan aiki don inganta tsaro a kan titin.

Egbetokun ya kuma jaddada cewa daukar matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa da fasijoji.

Ya kara da cewa ganin yawan jami’an tsaron a kan hanyar zai rage ayyukan ‘yan bindigar da ke kai hari.

Babban sifeton ya yi kiran hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummar garuruwan da ke yankin.

Karanta wannan: Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara wani asibiti a Jigawa

Ya kuma shawarci mutane su rika lura da shige da ficen mutane a garuruwansu, tare da kai rahoton duk wani mutum da ba su yarda da shi ba.

Ya ce ya kamata jama’ar garuruwan su rika hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankunansu da na fasinjojin da ke bin hanyar.

Matakin na zuwa ne kwanaki bayan wasu rahotnni sun ce ‘yan bindiga sun tare hanyar a kusa da garin Rijana inda suka sace fasinjoji masu tarin yawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here