An cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a Kano

FB IMG 16774182957648480
FB IMG 16774182957648480

Hukumar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa an cinna wa ofishin hukumar zaɓe ta ƙasar reshen ƙaramar hukumar Takai wuta.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

‘Ƴan banga ne suka cinna wa janareton da ake aiki da shi a cibyar wuta, lokacin da suka shiga wajen ta baya, amma ba wani ci ta yi ba, kuma an kashe ta, tuni muka ƙara yawan jami’anmu a wajen,’ in ji Kiyawa.

BBC ta tuntuɓi wani ganau wanda ya ce an cinna wutar kuma ta ƙona wasu robobi da aka zuba takardun ƙuri’un da aka ƙada amma ba ta ƙona wajen da ake aikin ƙirga ƙuri’u ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here