Wani kwamitin bincike na shari’a da gwamnatin Jihar Sokoto ta kafa ya gano cewa an karkatar da sama da Naira Biliyan 117 a tsawon shekaru takwas na mulkin tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Kwamitin, wanda ya miƙa rahotonsa a ranar Talata, ya kuma bayyana rashin bin ƙa’idojin aiki yadda ya kamata, karya dokokin kuɗi da kuma amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba a lokacin mulkin tsohon gwamnan.
Yayin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Mai shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga mai ritaya, ya bayyana cewa an kafa binciken ne domin tantance ayyukan gwamnatin da ta gabata ta hanyar takardun da za a iya tabbatarwa da kuma shaidu da aka rantsar, bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da muradun jama’a.
Ya bayyana cewa sakamakon binciken ya nuna manyan matsalolin kuɗi da suka kai sama da Naura Biliyan 117, waɗanda aka danganta su da raina dokokin saye-saye, raunin tsarin kula da kuɗi, da kuma amfani da ikon zartarwa ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Pindiga ya yi bayanin cewa an tsara rahoton zuwa manyan sassa biyar, waɗanda suka haɗa da tarihin binciken, shaidu da aka karɓa, cikakken sakamakon bincike, shawarwari, da kuma taƙaitaccen ƙarshe domin jagorantar matakan da gwamnati za ta ɗauka.
Ya ƙara da cewa kwamitin ya duba takardu, kwangiloli da bayanan kuɗi, tare da sauraron shaidu daga ma’aikatu, sassa da hukumomi masu alaƙa, da kuma sauran masu ruwa da tsaki da suka shafi gwamnatin da ake bincika.
Shugaban kwamitin ya yaba wa mambobin kwamitin kan jajircewa, ƙwarewa da gaskiyar da suka nuna, yana mai cewa an gudanar da aikin ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.
Ya kuma gode wa jama’a da cibiyoyin da suka bayar da haɗin kai, yana mai cewa gudunmawarsu ta taimaka wajen samar da rahoton da zai amfani Jihar Sokoto na dogon lokaci.
Ya kuma bayyana cewa miƙa rahoton ya yi daidai da ƙoƙarin ƙasa baki ɗaya na ƙarfafa alhakin shugabanci, kyakkyawan amfani da dukiyar jama’a, da ƙarfafa amincewar ’yan ƙasa ga tsarin mulki.
Yayin karɓar rahoton, gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya gode wa mambobin kwamitin kan jajircewa da sadaukarwar da suka nuna wajen aiwatar da wannan aiki mai sarkakiya.
Gwamnan ya jaddada cewa kafa kwamitin ba wai don ramuwar gayyar siyasa ba ne, sai dai bisa nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora da kuma amanar jama’a. Ya bayyana cewa an umurci kwamitin ne da tantance gaskiya da duba bayanai da shaidu bisa hujjoji kawai.
Sai dai gwamnan ya bayyana cewa za a kafa wani kwamiti domin fitar da takardar matsaya ta gwamnati kan rahoton, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da wannan tsari cikin gaskiya da adalci ga dukkan mutanen da aka ambata a cikin sakamakon binciken.













































