Dantata Bai Goyi Bayan Kowanne Dan Takara Ba – Sakatarensa

1678788480964
1678788480964
Sakatare ga fitaccen Attajiri a jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, mai suna Mustapha Abdullahi Junaid, ya musanta labarin da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta, cewa Dantata ya goyi bayan wani dan takarar kujerar gwamna a jihar Kano.
A karshen makon jiya ne aka samu jita-jitar cewa, Dantata ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, kafin daga bisani a gano cewa babu kamshin gaskiya a cikin labarin.
“Ina sanar da mutane cewa Aminu Alhassan Dantata bai ce azabi Gawuna ba, kuma bai ce azabi kowa ba, domin shi Uba ne a wajan kowa, saboda haka masu yada wannan jita jita sudaina kuma suyi gaggawa wajan cire post din da sukayi.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here