Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Majalisar Tarayya Ruwa a Jallo 

Yakubu Shehu 750x430.jpeg
Yakubu Shehu 750x430.jpeg

Rundunar ‘yan sanda ta ayyana neman mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Bauchi, Yakubu Shehu, ruwa a jallo.

Channels tv ta rahoto cewa ‘yan sanda na neman Yakubu duk inda ya shiga su damƙe shi bisa zargin kisan kai, haɗa baki, illata mutane da kuma gurɓata zaman lafiya.

Wannan ci gaban na ƙunshe ne a wata takarda da aka raɗawa CRO Form 5, wacce ta fito daga Ofishin Sufeta Janar na rundunar ‘yan sandan ƙasar nan.

Rundunar tsaron ta bukaci duk wanda ke da sahihan bayanan inda ɗan majalisar ya shiga ya tuntube ta, kuma ta yi alƙawarin ba da ladan miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka aka cafke shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Bauchi, Ahmed Wakil ne ya fitar da takarda ta musamman da ta ayyana neman ɗan majalisar ruwa a jallo.

2 SHARHI

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here