Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da laifukan kuɗi EFCC ta kama fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Samha M.Inuwa, bisa zargin wulaƙanta kuɗin Naira.
Sashen hukumar EFCC na shiyyar Kano ya bayyana cewa an kama Samha Inuwa ne biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ganta tana goge majina daga hancinta da takardun kuɗin Naira ,a bayyane.
Bayan yaɗuwar bidiyon, hukumar ta fara ɗaukar mataki ta hanyar gano inda take tare da kama ta domin amsa tambayoyi dangane da lamarin.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a halin yanzu ana tsare da ita a cibiyar tsarewa ta hukumar EFCC yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Hukumar ta bayyana cewa da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar shari’a.













































