Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara

Osinbajo 678x381 1
Osinbajo 678x381 1

A Litinin ɗin nan ne mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa na baɗi.

“A yau, cikin tawali’u, a hukumance na bayyana aniyata ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a tarayyar Najeriya a jam’iyyar APC,” in ji shi a wani faifan bidiyo.

Sanarwar ta Osinbajo dai ta kawo ƙarshen cece-ku-ce da aka yi na tsawon watanni a kan sha’awar sa ta takarar shugaban ƙasa a 2023 tare da ƙara yawan masu neman muƙamin.

Hakan kuma ya sanya shi yin arangama kai tsaye da tsohon ubangidansa a jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna sha’awarsa a farkon shekarar.

A jawabinsa na bayyanawa, Osinbajo ya ce, ya jajirce wajen ci gaba da manufofin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

“Idan da yardar Allah da yardar jama’a aka ba ni dama, to na yi imanin cewa da farko, dole ne mu kammala abin da muka faro, tare da sauya fasalin tsarin tsaro da leken asiri,” in ji shi, “mu kammala gyara. na tsarin adalcinmu da mayar da hankali kan isasshen albashi da jin walwalar ma’aikatan shari’a da tabbatar da adalci ga kowa musamman masu bin doka da kuma  sauri inganta ayyukanmu na samar da ababen more rayuwa, musamman wutar lantarki, tituna, layin dogo, da hanyoyin sadarwa na zamani, samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa don bunƙasuwa, da bunƙasa harkokin noma zuwa mataki na gaba, musamman injiniyoyi da bunƙasa ta da ƙara inganta harkokin fasahar ƙere-ƙere da za ta samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan Nijeriya; inganta shirin mu na saka hannun jari na zamantakewa, zuwa cikakken shirin jin dadin jama’a.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here