Dala 1 ta rufe akan Naira 417 a kasuwannin chanji farashin Gwamnati

Naira, Dala, CBN, BDC, sayar, karyata
Sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Facebook da X (Twitter) da ke ikirarin cewa ana musayar Dalar Amurka tsakanin Naira 900 zuwa...

Darajar Naira ta yi kasa da digo 8 ranar Litinin a kasuwar canji farashin Gwamnati dana masu masana’antu da Gwamnatin ta basu damar sayar da Dala, inda aka chanjar da Dala 1 kan Naira 417, maimakon Naira 416 da Kobo 17 da aka sayar da Dalar a ranar Juma’a.

Canjar da Dala 1 kan Naira 444 shi ne mafi girman farashin da aka samu a kasuwannin ranar kafin daga bisani ya daidaita kan Naira 417, yayin da aka sayar da farashin kasa da Naira 410 duka dai a kasuwar ranar.

A ranar Alhamis kuwa an sayar da jimillar dala miliyan 127 da Dala dubu 12 a kasuwannin juba hannayen jari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here