A cikin wannan bincike, ELIJAH AKOJI ya bankado yadda aka gudanar da almundahana wajen aiwatar da ayyukan samar da ruwa na sama da Naira miliyan 490 a Gasuha da ke karamar hukumar Bade a jihar Yobe, wanda ma’aikatar albarkatun ruwa ta bayar a shekarar 2020.
Aikin yana nan ne a gundumar mazabar shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan a Yobe ta arewa.
A shekarar 2020, Gwamnatin Tarayya ta hannun Asusun bada tallafin Gaggawa na Covid-19, ta yi ikirarin aiwatar da ayyuka daban-daban guda 14 ta hannun Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, da suka kai Naira samada Naira Miliyan dubu 2.
Daya daga cikin irin wadannan ayyuka shine aikin samar da ruwa na GARIN GASHUA. Gasuha babbar gundumar siyasa ce a karamar hukumar Bade ta jihar Yobe- mahaifar Sanata Ahmed Lawal, shugaban majalisar dattijai na majalisa ta 9.
Bayanai sun ce ta cikin asusun gaggawa na Covid-19, cikin 2020 Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya ta ba kamfanin Yubar Consultants Ltd, kwangilar samar da aikin ruwan a Gasuha.
An tsara kammala aikin ne cikin kwanaki 120. Amma bayan shekaru biyu, akayi watsi da shi ta yadda ciyayi suka mamaye wurin.
Jaridar SOLACEBASE ta gano cewa an bayar da aikin samar da ruwan ne a kan kudi Naira miliyan 492,634,237 ta hanyar biyan kudin karakakaf.
Aikin samar da ruwan a Gasuha na miliyoyin naira ya kamata yayi ya kawo karshen matsalar kamfa da karancin ruwan da al’ummar yankunan ke fuskanta tare da samar musu da ruwan sha dan cin gajiyar mulkin dimokuradiyya.
Binciken da Solacebase tayi ya nuna cewa babu ko da rijiyar burtsatse guda daya a kusa da garin Gasuha da akayi amadadin wadancan madudan kudade.
Kamar yadda Jaridar Solacebase ta gano, wani kamfani ne na dangin Umar Barambu, wanda tsohon dan jam’iyyar APC ne mai wakiltar mazabar Akko a majalisar wakilai ta tarayya.
Barambu ya sha kaye a zaben 2015, bayan Shan kaye ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP inda a yanzu ya tsaya takara sake neman waccan kujera.
Wurin Aikin ya surkume da ciyawa duk da cikakken kudin da aka biya dan wannan kwangila.
Wakilinmu da ya ziyarci wurin da aka gudanar da aikin tare da rakiyar wasu al’umma inda ya tarar da ciyawa ta mamaye wurin. Babu kuma wata shaida dake nuna alamun ana wani aiki a gurin.
Mazauna yankin sun shaidawa Jaridar Solacebase cewa an kulle wurin tun farkon wannan shekarar ba tare da wani aiki ba.
A titunan garin, kamar yadda aka saba ganin samari masu shekaru daban-daban na tura amalanken Ruwa da jarkokin ruwa domin sayarwa mazauna garin suna neman ruwan sha.
Daga Katuzu zuwa Kuratandu, Filin Tanda zuwa kurkukun Bayan, da kuma unguwannin Takari Zarigo, wakilin namu ya kirga rijiyoyin burtsatse guda 8 da allunan da ke nuni da cewa ma’aikatar albarkatun ruwa ne karkashin kulawar Sanata Ahmed Lawal da Yubar Consultancy Ltd ta gina su.
Haka kuma, wakilan namu sun kirga rijiyoyin burtsatse sama da 19 wadanda dukkansu ba sa aiki kwata kwata, lamarin da ya sa mazauna yankin ke dogaro da rijiyoyin burtsatse aboye da wasu mazauna yankin suka samar don yin kasuwanci.
Wannan shi ne abin bakin ciki ga al’ummar Gasuha, al’ummar da ke da mazauna sama da miliyan daya.
“Aikin da ake kira aikin samar da ruwan sha da suka fara tun awatan agusta shekarar 2020, idan har za su iya gyara rijiyoyin burtsatse da ba su da aiki ta hanyar amfani da kayan aiki masu inganci, ba na jin mutanen yankunan za su bukaci wani aikin samar da ruwa irin wannan.
Yayin da wakilin mu ke kokarin zantawa ba Danangila, yana ta faman yimasa hanya hanya Dan kaucewa fada mar gaskiyar lamarin, inda daga bisani ma yayi shiru abinsa.
Jaridar Solacebase ta tuntubi dan kwangilar don tabbatar da halin da aikin yake ciki duk da cewa ya karbi sama da Naira miliyan 496, amma bai ce komai gameda halin da aikin ke ciki ba.
Abubakar Barambu, daya daga cikin daraktocin kamfanin Yubar Consultants Ltd, bayan tuntubar sa, ya bukaci a ba shi lokaci kafin ya maida martani ga wakilin namu. Saidai a lokacin da aka sake tuntuɓar sa bayan mako guda, se ya ƙi cewa komi.
Amma da Jaridar Solacebase ta tuntubi ma’aikatar don neman cikakkun bayanai game da aikin, ma’aikatar ta bukaci abata lokaci don tattara bayanai. Saidai duk da baiwa ma’aikatar makonni biyu amma bayan sake tuntubar ta, ba ta bada wani bayani ba.
A halin da ake ciki, ayyukan Naira miliyan 400 sun lalace tareda yin 6atan dabo a Gashua da ke karamar hukumar Bade sakamakon gazawar da dan kwangilar ya yi na kammala shi duk da biyan sa da akayi batare da bin ko da sisin kobo ba.












































