Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ziyarar da ya kai wa tsohon ubangidansa, Cif Olusegun Obasanjo a ranar Litinin ba ta shafi siyasa ba, illa kawai ziyarar gaisuwa ce ga tsohon shugaban kasar.
Atiku wanda ya isa gidan Obasanjo na Abeokuta dake cikin harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo da misalin karfe 12:37 na rana, ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Sanata Liyel Imoke, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, Sanata Abdul Ningi, da dai sauransu.
Atiku, tare da ‘yan tawagarsa, sun samu tarba a gidan Obasanjo daga hannun dattijon jihar, Otunba Oyewole Fasawe, kafin daga bisani su yi wata ganawar sirri da Obasanjo wanda ya dauki kusan awa daya da rabi.
Labari mai alaƙa: Atiku, Tambuwal, da sauran su na ganawar sirri da Obasanjo a Abeokuta
Da yake fitowa daga taron da misalin karfe 2:17 na rana, Atiku ya shaidawa ‘yan jarida masu cewa ya kai ziyarar ban girma ga tsohon ubangidan nasa ne ba wai ya tattauna batun siyasa ba.
Da aka tambaye shi makasudin taron da kuma ko yana da alaka da burinsa na shugabancin kasa a 2027, Atiku ya ce: “Na zo ziyarar ban girma ne ban zo na nan don yin maganar siyasa ba”.
“Ban je Abeokuta don ganin Obasanjo ba saboda siyasar 2027,” in ji shi, yana mai bayyana taron a matsayin “ziyarar girmamawa ce kawai”.
Kokarin da Tambuwal ya yi don jin ta bakinsa a kan jigon ziyarar ya ci tura, domin shi ma ya ki yin magana kan dalilin ziyarar.