Atiku, Tambuwal, da sauran su na ganawar sirri da Obasanjo a Abeokuta

Atiku Obj 750x430

A yanzu haka tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana ganawa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Atiku, wanda ya isa gidan Obasanjo da ke cikin harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL) da misalin karfe 12:37 na rana a yau Litinin, ya samu rakiyar tsaffin gwamnonin jihohin Sokoto da Cross Rivers, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Liyel Imoke, da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya.

Da isar Atiku tare da ‘yan tawagarsa sun samu tarba a gidan Obasanjo daga Otunba Oyewole Fasawe, kafin daga bisani su shiga wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar, wanda ke jiran masu ziyarar sa.

Ko da yake har yanzu ba a samu cikakken bayanin ganawar ta su ba.

Karin bayani na tafe…..

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here