Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG), Umar Farouk Ibrahim wanda aka nada.
SolaceBase ta ruwaito cewa Umar Farouk Ibrahim ya maye gurbin Dr. Abdullahi Baffa Bichi, wanda aka sauke shi daga mukamin SSG saboda rashin lafiya.
Karin karatu: Gwamna Abba ya cire kwamishinoni biyar da SSG da Sagagi
Bikin wanda ya kasance karamin taro a ofishin gwamna, babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano Barr Haruna Isa Dederi ya jagoranci rantar da shi.