Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sakin dala miliyan 8.5 ga ma’aikatar kula da jin kai da ci gaban al’umma domin a samu saukin kwashe ‘yan Najeriya da ke Ukraine biyo bayan yaki da kasar ke gwabzawa da Ukraine.
Umurnin ya biyo bayan amincewa da takardar hadin gwiwa da aka gabatar wa majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Da take yi wa manema labarai karin haske bayan kammala taron majalisar, ministar, Hajiya Sadiya Umar Farouk, tare da karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada, sun ce kudin ne za a kwashe akalla ‘yan kasar 5,000 da suka makale a sakamakon rikicin.
Ambasada Dada ya bayyana cewa, an baiwa kamfanonin jiragen sama na Air Peace da Max Air kwangilar samar da jirage guda uku tare da gudanar da ayyuka da dama domin saukaka tashin jirgin.













































